
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano, PCACC ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan badaƙalar Naira miliyan 440 da ake zargin sauya akalarsu.
Kuɗin wanda aka turo Naira miliyan 10 daga asusun kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar, an tura su ga wani kamfanin magani mai suna ‘Novomed Pharmaceuticals’ na Musa Garba Kwankwaso, ɗa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A halin yanzu dai hukumar ta fara gudanar da bincike kan sayan magani daga kamfanin sakamakon saɓa wa dokokin gudanarwar al’umma.
Wata takarda da PCACC ta fitar da ke ɗauke da kwanan wata kamar haka; 18 ga watan Yuli, 2024 ta gayyaci manyan jami’an ma’aikatar ƙananan hukumomi ta jihar don yin bincike akan su kan cinikin.
Haka na zuwa ne bayan da wani shahararren ɗan soshiyal media, Dakta Bello Galadanchi ya shiga tona asirin jagorori a Najeriya kan ayyukan da su ka shafi badaƙala.
Galadanchi ya zargi gwamnatin Kano da sauya akalan kuɗaɗen da aka ware ne don sayan magani daga kamfanin Novomed Pharmaceuticals wanda hakan ya yi sanadiyyar zargin karkatar da Naira miliyan 10 daga kowace ƙaramar hukuma.
A lokacin da ya ke magana, gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar, ya musa batun zargin sauya akalar kuɗaɗen, ya na mai cewa gwamnatinsa ta na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta toshe duk wata kafa da zata bada damar ɓarnatawa ko karkatar da dukiyar al’ummar jihar.
