
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta samar da wani shirin bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar bayar da Naira biliyan 200 don a raba wa manyan kamfanoni guda 75 da masana’antu ƙanana da tsaka-tsaki (MSMEs) a matsayin rance.
Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba hannun-jari, Doris Uzoka-Anite ta faɗi hakan a jiya Litinin, inda ta ce hukuncin wani mataki ne na sake farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa da gwamnatin ta ɗauka.
Ta kuma ce, za a bai wa kowane ɗaya daga cikin manyan kamfanoni 75 Naira biliyan ɗaya a matsayin aro wanda za a fara daga watan Satumba, 2024.
Sauran biliyan 125 kuma za a raba a tsakanin masu ƙanana da tsaka-tsakin masana’antu don su bunƙasa harkokin kasuwancinsu.
Ministar ta ƙara da cewa, sama da ɓangarori 700,000 da aka tantance su ne ke neman amfana daga cikin shirin wanda nan ba da jimawa ba za a fara rabawa.
A lokacin da ta kai ziyara wa gwamnan jihar Cross-River, Bassey Otu, Uzoka-Anite ta samu tattaunawa da waɗanda su ka amfana da shirin bayar da tallafi da aron kuɗi na shugaban ƙasa inda ta bayyana cewa hakan ƙoƙari ne na gwamnati wajen inganta rayukan al’umma tare da ƙara kusanto da su ga gwamnati.
Kawo yanzu, aƙalla sama da mutane 660,320 masu ƙaramin ƙarfi ne su ka amfana da tallafin Naira 50,000 ga wannen su cikin ƙananan hukumomi 774 na faɗin Najeriya wanda hakan ke wakiltar kaso 60 na mutane miliyan ɗaya da ake fatan tallafin ya kai gare su inda a halin yanzu ake cigaba da tantance su.
Kazalika, a ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da adalci, ta ce akwai buƙatar jagororin al’umma da ƙungiyoyinsu su sanya ido don tabbatar da tallafin ya kai lungu da saƙo na sassa Najeriya.
