Masu zuba hannun jari na ƙasar China ‘Zhongshang Industrial Investment’ sun cigaba da shirin su na sayar da gidajen baƙi guda biyu na gwamnatin tarayya da ke birnin Liverpool a ƙasar Ingila.
Masu sayarwar na shirin fara tallata gidajen a manhajar eBay in da ake hada hadar kasuwanci.
Wannan dai ya biyo bayan hukunci wata kotu a Faransa, in da kamfanin ke neman gwamnatin Nijeriya da biyan kusan dala miliyan 70. Wannan ya biyo bayan wata yarjejeniya da gwamnatin jihar Ogun ta yi da kamfanin lokacin tsohon gwamnan Amosun.
Duk da irin ƙoƙarin da gwamnatin Nijeriya ke yi, kamfanin ya cigaba da ƙara a kotu domin bashi damar sayar da wasu kadarorin gwamnatin da ke ƙasashen Belgium, Faransa da sauran su.
Shawarar sayar da gidajen a dandalin eBay, ya biyo bayan yunƙurin sayar da gidajen da ake son yi a buɗe saboda gudun zargin da zai iya biyo baya.
