
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar malamai ta Ƙasa, NUT ta aika da saƙon umarni ga malamai a faɗin Najeriya kan cewa su kasance cikin shirin tafiya yajin aiki matuƙar ƴan sanda su ka kama shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero.
Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sandan ta aika wa Ajaero saƙon gayyata a ranar Litinin don ya zo ofishinta a washe gari kan zargin sa da hannu acikin laifukan ɗaukar nauyin ta’addanci, zamba cikin aminci da sata ta yanar gizo inda ta ce matuƙar bai amsa kiran nata ba, to za ta kama shi.
Sakamakon haka ne NUT ta fitar da wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun shugabanta, Audu Amba da na sakatarensa, Abdullahi Mohammed kan cewa mambobinta su zauna cikin shiri.
NUT ta ce yunƙurin kama Ajaero cin mutunci ne a gare su da kuma ƙoƙarin daƙile ƙarfin faɗa a-aji na ma’aikata a Najeriya.
Kazalika, ta ce Majalisar Zartarwa (NEC) ta NLC ta gudanar da taro tare da ɗaukar matakan kare kima da cin gashin kai na ƙungiyar ƙwadago a Najeriya wanda daga cikin su ta umarci rassanta su shirya wa tafiya yajin aiki.
