Ofishin Shugaban Ƙasa ya magantu kan matsayin jirgin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

La’akari da sarƙaƙƙiya da ke tattare da tafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi zuwa Farisa a wani sabon jirgi mai suna A330, offishin shugaban ƙasa ya yi cikakken bayani game da jirgin.

Mai taimaka wa Tinubu na musamman kan harkokin yaɗa labaran jaridu, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce jirgin ba sabo ba ne wanda an yi amfani da shi kafin ofishin ya mallake shi sannan daga baya aka saye shi ta hanyar wani banki akan tsarin sayar wa wanda ya fi biyan kaso mai tsoka daga cikin waɗanda aka tallata wa.

Cikin wata hira da jaridar BBC Hausa, Abdulaziz ya ce asalin jirgin mallakar larabawa ce wanda daga bisani gwamantin Najeriya ta saye shi.

Gwamnatin Tarayya ta nemi sayan jirgin ne sakamakon wani bincike da Majalisar Dokoki ta yi akan tsohon jirgin Fadar shugaban ƙasa ƙirar Boeing B737-700 da ya ɗauki shekaru 19 ya na hidima wa Fadar wanda a sanadiyar haka ne Majalisar ta ke ganin ƙarfinsa ya gaza wajen gudanar da harkokin tafiye-tafiye cikin ƙoshin lafiya.

Sannan, ya bayyana cewa kuɗaɗen da aka sayi jirgin, an cire su ne daga asusun ajiyar kuɗin ayyukan da ka iya bijirowa ba asalin asusun kasafin kuɗin ƙasa ba.

By Babaji