Gwamnonin hamayya da ba su raba tallafin gwamnati ba su ka assasa zanga-zanga

Spread the love

Wata ƙungiyar da ake kira ‘Apostles of Jagaban’ sun zargi gwamnoni daga jam’iyyun hamayya da rashin raba tallafin da gwamnatin tarayya ke bayarwa a jihohin su.

Shugaban ƙungiyar, Cif Gilbert Olukususi a wata sanarwa da ya bayar ya zargi gwamnonin da karkatar da ta tallafin shinkafa da gwamnatin tarayya ta bayar domin a rabawa a al’ummar su.

Shugaban ya zargi gwamnonin da rashin yin hakan, shi ya ƙara tunzura zanga-zangar matsin rayuwa da a ka gudanar a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa, da irin wannan zanga-zangar su ka fake ɓatagari su ka shiga domin har su ka lalata dukiyoyin gwamnati da na al’umma.

By ukarofi