Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tafiyar da harkokin ƙasar tamkar sana’ar iyali.
Atiku a wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, a ranar Larabar da ta gabata, ya yi zargin cewa, Shugaba Bola Tinubu, da iyalansa, da wasu makusantansa ne ke tafiyar da makomar ‘yan Nijeriya.
Ya ce ya yi imanin cewa ko bayan Mista Tinubu ya bar ofis, karya wadannan sarka ba zai yi wuya ba.
Atiku ya kwatanta yadda Tinubu ya yi cudanya da sana’o’insa na kasuwanci a Legas da kokarinsa a matakin tarayya.
“Kamar yadda Alpha Beta, Primero, da sauran su ke zama a matsayin ‘yan amshin shatan Tinubu a Legas, suna tafiyar da muhimman sassa da kuma samar da kuɗaɗen shiga ga shi da iyalinsa, ya fara yin kwafin hakan a matakin tarayya,” in ji shi.
Ya bayyana mamakinsa da yadda kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC Ltd) ke gudanar da ayyukansa da kuma yadda kamfanin mai na gwamnati ya sanya hannun jarinsa a ƙarƙashin OɓH, kamfanin da Oando ƙarƙashin jagorancin Wale Tinubu, ɗan uwa ne ga shugaban ƙasar, ya mallaki kashi 49 cikin 100.
Sanarwar ta ce Atiku ya yi nadamar cewa aniyarsa ta mayar da kamfanin NNPC a matsayin wani kamfani da kuma ƙara bayyana gaskiyarta ta ci karo da abin da ya bayyana a matsayin “samun satar NNPC da wasu jiga-jigan masu rike da muƙamai a kusa da shugaban ƙasar ke yi.”
