Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ayyana haramta, shirin biyan kuɗin fakin na motoci, wanda aka fi sani da Park and Pay a babban birnin tarayya Abuja.
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai kai tsaye a ranar Laraba a Abuja a wani ɓangare na cikarsa shekara guda kan karagar mulki.
Shirin wanda aka fara ɓullo da shi kimanin shekaru goma da suka wuce, an dakatar da shi ne biyo bayan ƙorafe-ƙorafen jama’a. Sai dai an sake dawo da shi a watan Agustan bara, kwanaki kaɗan kafin Wike ya hau kujerar minista.
Ministan wanda shi ma ya fusata kan tsarin rabon da ake tura wa gwamnatin, ya bayyana cewa yayin da mai ba da shawara ke ɗaukar kashi 80 cikin 100 na abin da aka samu, Hukumar FCT ta ɗauki sauran kashi 20 cikin 100.
A cewarsa: “Ba na nan, wani abokin aikina, abokina ya kira ni, shi babban lauyan Nijeriya SAN ne. Ya ce, ‘Yallaɓai, mutane sun zo ofishinmu a yanzu suna ƙoƙarin sace mana dukkan motocinmu kuma sun ce daga Sakatariyar Sufuri ne. Na ce, mene ne wannan? Na ce a ba wa mutumin wayar. Na ce kai wane ne ya ce daga Park and Pay. Na ce me kake nufi da Park and Pay? Ina parking a gidana na biya?
“Na kira Sakataren Sufuri na Mandate. Na ce, zo, wa ya gabatar da Park and Pay? Me ake nufi? Wanene yake karɓar kuɗin?
“Ba mu sani ba, an yi yarjejeniya tsakanin Sakatariyar da wasu da ke cewa mashawarta ne. Masu ba da shawara? Na ce to, consultant yana ɗaukar kashi 80, gwamnati kuma ta ɗauki kashi 20? Na ce lafiya, a ina ake biyan wannan kuɗin? Na ce, rubuta wata sanarwa kuma a kira Daraktan yaɗa labarai, a aika da sanarwar cewa jama’a su sani cewa babu wani abu da ake kira Park and Pay. Don haka, a wasu lokuta, ana yin waɗannan abubuwa ne da gamsuwa da Sakatarorin daban-daban. Ni gwamna ne. Don haka, na san cewa waɗannan abubuwan suna faruwa kuma ba za mu musanta hakan ba,” in ji shi.
