Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata uwa ta zama mutum ta farko da aka ɗaure a gidan yari a ƙarƙashin dokar auren dole a ƙasar Ostireliya, saboda ta umurci ’yarta ta auri mutumin da zai iy kashe ta.
Sakina Muhammad Jan, mai shekaru 40 da haihuwa, an same ta da laifin tursasa Ruƙia Haidari ta auri Mohammad Ali Halimi mai shekaru 26 a shekara ta 2019, domin ta samu wasu kuɗaɗe.
Bayan makonni shida da ɗaurin auren, Halimi ya kashe sabuwar amaryar tasa – laifin da ya sa aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
A ranar Litinin, Jan – wanda ta ƙi amsa laifinta – an yanke mata hukuncin ɗaurin aƙalla shekara guda a gidan yari, saboda abin da alƙali ya kira “tursasa aure” da ta yi wa ‘yarta.
An gabatar da dokokin auren dole a Ostiraliya a cikin 2013 kuma suna da hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari. Akwai ƙararraki da dama a kan wannna batu, amma Jan ita ce mutum ta farko da aka yankewa hukunci kan laifin.
Wata ‘yar gudun hijirar Hazara ta Afganistan wacce ta tsere daga zalunci daga Taliban kuma ta yi hijira zuwa yankin ɓictoria tare da ‘ya’yanta biyar a cikin 2013, lauyoyin Jan sun ce tana fama da “bakin ciki” game da mutuwar ‘yarta amma ta ci gaba da tabbatar da cewa ba ta da laifi.
