Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya sake kai wa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu burinsa, a wannan karon kan ci gaba da biyan tallafin man fetur.
Wannan sukar ya biyo bayan amincewar da Tinubu ya yi a kwanan baya ga buƙatar Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) na yin amfani da rabon 2023 saboda Tarayyar ta ba da tallafin mai.
Wannan matakin ya haifar da damuwa musamman daga Atiku, wanda ya bayyana rashin jin daɗinsa a wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar.
Ya bayyana ci gaban da aka samu a matsayin wani misali na shugabanci mara kyau a ƙarƙashin wannan gwamnati mai ci.
Atiku ya yi nuni da cewa matakin na Tinubu ya ci karo da furucin da shugaban aasar ya yi tun farko a kafar yaɗa labaran aasar, inda ya sanar da kawo aarshen tsarin tallafin man fetur.
Tsohon mataimakin shugaban aasar, wanda kuma shi ne ɗan takarar shugaban aasa na jam’iyyar PDP a zaɓen da aka gudanar a baya-bayan nan, ya bayyana cewa tun kafin wannan sanarwar, an dage da nuna cewa an dawo da kuɗaɗen tallafin ta hanyar da ba ta dace ba.
“Bambancin da ke tsakanin kalaman shugaban kasa da ayyukansa ba wai kawai na zubar da mutuncin shugabancinsa ba ne, har ma yana zubar da mutuncin gwamnatinsa,” inji Atiku.
Baya ga sukar da ya yi kan manufar tallafin, Atiku ya yi Allah-wadai da jinkirin da aka samu wajen sake gudanar da aikin matatar man Fatakwal, inda ya bayyana hakan a matsayin abin kunya a ƙasa.
Ya danganta wannan gazawar da ke faruwa a kan Shugaba Tinubu, wanda kuma yake riƙe da muƙamin Ministan Albarkatun Man Fetur.
Atiku ya kuma ƙara da cewa, ci gaba da musantawa da kamfanin NNPC ya yi, ya ƙara dagula ƙalubalen da ‘yan Nojeriya ke fuskanta, waɗanda ke fama da ƙarancin man fetur da tsadarsa.
Ya nuna damuwarsa kan shirun da Shugaban ƙasar ya yi a yayin da ake ci gaba da cece-kuce tsakanin masu zuba jari na cikin gida da ke tallafa wa ayyukan matatar man da kuma masu ƙoƙarin shigo da man fetur.
A ƙarshe Atiku ya yi kira ga shugaba Tinubu da ya ɗauki kwakkwaran mataki domin warware waɗannan muhimman batutuwan da suka shafi muradun kasa. Ya jaddada buƙatar yin gaskiya cikin gaggawa a ɓangaren albarkatun man fetur sannan kuma ya buƙaci hukumar da ta fayyace irin sarƙaƙiyar da ke tattare da manufofin tallafin da kuma tace man fetur.
