Daga MAHDI M. MUHAMAMD
Hukumar da ke kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki da abokan hulɗa ta ƙasa, FCCPC, ta rufe kamfanin ruwa na Fabsi da ke Kubwa, Babban Birnin Tarayya, biyo bayan ƙorafin da masu amfani da shi suka yi na amfanin da lalatattun robobi masu ɗauke da ƙwayoyin cuta.
Hukumar, a hukumance ta shafinta na ɗ ranar Juma’a, ta ce bincikenta ya gano gagarumin keta ƙa’idojin kariya na masu amfani da kamfanin.
FCCPC ta ce, Fabsi ya gaza samar da muhimman bayanai, gami da kwanan watan samarwa, kwanakin ƙarewa, da lambobin batch a kan samfuran nasa.
Hukumar ta ce, kamfanin ba shi da muhimman bayanan bin ƙa’idojin da suka dace don tabbatar da aminci da ingancin samfuran.
“Fabsi Table Water ya yi ikirarin tsawon watanni biyu don kayayyakin sa, duk da haka rashin samarwa da lokacin karewa ya sa wannan da’awar ba ta tabbata ba.
“Kamfanin ya danganta watsi da wannan muhimman bayanai da ƙalubalen buga ruwa, wanda FCCPC ke ganin ba za a amince da shi ba.
“Madaidaici kuma cikakke lakabin samfurin shi ne ainihin abin da ake buƙata a ƙarƙashin ƙa’idodin da suka dace,” inji hukumar a kan ɗ.
FCCPC ta ce, ta dakatar da ayyukan kamfanin na wani ɗan lokaci tare da kira ga mahukuntan kamfanin domin gudanar da bincike.
