Daga MAHDI M. MUHAMMAD
An tsinci gawar wata budurwa mai suna Mojisola Awesu, ɗalibar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara.
Budurwar mai shekara 21 da aka bayyana ɓacewarta tun ranar 9 ga watan Agustan 2024, an same ta babu rai a wani wajen zubar da shara da ke unguwar Aleniboro a Ilorin, babban birnin jihar.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.
Kakakin rundunar, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa marigayiyar ta samu kiran waya daga wata Mis Timileyin a ranar 9 ga watan Agusta, 2024, game da wani taron da ɗaliban makarantar a Offa, da suka shirya.
Matar ta gabatar da marigayiyar ga wani Adebayo Happiness, ɗaliban Jami’ar Summit, wanda ake zargin ya gayyace ta zuwa sharholiyar dare a kan zargin cewa ta yi a matsayin budurwarsa kan kuɗi Naira 15,000.
“Duk da haka, marigayiya Mojisola ta sanarwa da abokiyar zamanta, wata Blessing O, cewa ta ji ba daɗi a otal ɗin da Adebayo Happiness ya sauke ta kuma ta lura cewa babu wani biki a wajen da aka ce.
“Ba daɗewa bayan wannan tattaunawar wayarta a kashe ta kuma duk ƙoƙarin da Miss Blessing ta yi na samunta bai yi nasara ba”, inji shi.
Ta ce, an kama wanda zargin da aikata kisan kuma an miƙa shi ga cibiyar binciken laifuka ta jihar.
