Daga MAHDI M. MUHAMMAD
An samu ƙarin bayanai kan kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da su ke da hannu wajen shigo da man fetur marasa inganci daga Malta, inda Sayyu Dantata, ɗan uwa ga shugaban rukunin Dangote Aliko Dangote na ɗaya daga cikin masu shigo da kayan.
A watan Yuli, Dangote ya yi zargin cewa wasu jami’an kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPC da dillalan mai suna haɗa masana’antun mai a Malta, inda suke tacewa da shigo da kayayyakin da ba a taɓa gani ba, waɗanda ake kawowa Nijeriya domin amfani da su.
Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan ikirarin da manajan daraktan hukumar haƙowa da sarrafa man fetur ta Nijeriya, NMDPRA, Ahmed Farouk ya yi na cewa kayayyakin da ake samu daga matatar man Dangote sun yi kasa da waɗanda ake shigo da su daga ƙasashen waje.
“Ko a gangan 650,000 da gangan 700,000, abin da muke samarwa ya fi wanda aka shigo da shi inganci. Kuma na tabbata mafi yawanku za su fuskanci matsaloli da ababen hawan ku saboda mugun man da aka shigo da shi ƙasar nan, har yanzu na tsaya kan abin da na faɗa.
“Jeka gidan mai, za ku iya karɓa ku duba ingancin. Wannan hanya ce mai sauƙi. Amma duk waɗannan wanda wani zai kawo jirgi, ya kawo takardun bogi. Wasu mutanen NNPC, wasu ’yan kasuwa sun buɗe wani kamfanin hada-hadar kuɗi a wani wuri a Malta. Duk mun san waɗannan wuraren, mun san abin da suke yi,” inji Dangote.
A halin da ake ciki, takardun da Jaridar NewsPoint ta samu sun bayyana cewa kamfanin man MRS na ɗaya daga cikin kamfanonin mai da ke shigo da mai daga Malta.
Jaridar ta tattaro cewa ɗan uwan Dangote – Sayyu Dantata – shi ne wanda ya kafa kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin man da iskar gas na MRS.
Sauran daraktocin MRS sun haɗa da, Aisha Dantata, Abdu Dantata, Patrice Alberti, GMD, Amina Maina, GCOO, da Mohammed Dantata.
Wasu daga cikin takardun da wakilin jarodar ya samu sun bayyana cewa, kamfanin ya shigo da mai zuwa Nijeriya ne a watan Fabrairun 2024 ta jirgin ruwa mai suna MT AETHER.
