An saka ranar fara sayar wa matatar man Ɗangote da ɗanyen mai a Naira

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alamu dai na nuna cewa ‘yan Nijeriya sun kusa samun sauƙi yayin da ake sa ran fara sayar da ɗanyen mai ga matatar man Dangote da sauran matatun mai na cikin gida a ranar 1 ga Oktoba, 2024.

Masu fashin baƙi sun ce sayar da ɗanyen mai ga matatun man ƙasar nan a Naira zai rage farashin man fetur ɗin sosai.

A cewar wani saƙo da aka wallafa a shafin ɗ na ma’aikatar kuɗi, sanarwar ta fito ne daga ganawar da ministan kuɗi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Wale Edun ya yi da kwamitin aiwatarwa a ranar Litinin a Abuja.

Taron dai an yi shi ne domin duba ci gaban da aka samu kan muhimman tsare-tsare.

Majalisar zartarwa ta tarayya a ranar 29 ga watan Yuli ta amince da ƙudirin Shugaba Tinubu na kamfanin NNPC na dakatar da sayar da ɗanyen mai ga matatun ƙasar cikin kuɗaɗen waje.

Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da bayar da ganga 450,000 da za a yi amfani da su a cikin gida a cikin Naira ga matatun man Nijeriya, ta hanyar amfani da matatar Dangote a matsayin gwaji.

An ɗauki matakin ne domin tabbatar da daidaiton farashin man fetur mai rahusa da kuma canjin dala da naira.

A martanin da ta mayar, ministam kuɗi ya ƙaddamar da wani ƙaramin kwamitin kwararru da aka ɗorawa alhakin samar da tsarin sayar da danyen mai ga matatun man ƙasar a cikin Naira.

Masu sa ido a masana’antu sun ce matatar Dangote za ta buƙaci jigilar ɗanyen mai guda 15 a duk shekara domin gudanar da aikin da ya dace.

By ukarofi