Gasar Kofin Duniya: An cire Messi daga cikin waɗanda za su buga wa Argentina wasannin fitar da gwani

Spread the love

Kamfanin Dillancin Labarai na ya bayyana cewa, AP Lionel Messi bai zai buga wa Argentina wasannin fidda gwani na neman gurbin shigar Gasar Kofin Duniya ba saboda raunin da ya ji.

Kocin Argentina Lionel Scaloni ya sanar da tawagar ’yan wasa mai qunshe da ’yan qwallo 28 a ranar Litinin.

Argentina za ta kara ne da Chile a ranar 5 ga watan Satumba, sai kuma kwanaki biyar bayan hakan ta kara da Colombia.

Shi dai Messi yana fama ne da rauni a kwaurinsa na dama.

Angel Di Maria mai shekaru 36 wanda ya yi ritaya daga bugawa qasarsa ta Argentina qwallo shi ma ba ya cikin tawagar.

Bayan da Argentina ta lashe kofin COPA America ne Di Maria ya sanar da yin ritaya.

Ita dai Argentina ita take riqe da kofin duniya wanda ta lashe a Qatar a shekarar 2022.

By ukarofi