Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, NFF, ta kusa kawo ƙarshen taƙaddamar da ake yi kan zaɓen wanda zai cigaba da jan ragamar horar da ’yan wasan Super Eagles na Nijeriya, duk da cewa har yanzu akwai tsaikon da ake fuskanta kan cire caya daga cikin mutane biyu da suka rage.
Tawagar Super Eagles ba ta da koci tun bayan da Finidi George ya ajiye aikinsa bayan wasa biyu kacal a cikin kwatiraginsa ta shekara biyu.
Finidi yana cikin ’yan wasan Nijeriya da suka lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (Afcon) ta shekarar 1994, sannan ya taɓa riƙe matsayin na riƙon ƙwarya a wasan sada zumunta a watan Maris.
Wasa ɗaya kawai ya samu nasara a cikin huɗu da ya jagoranci tawagar, sannan Benin ta yi nasara kan Nijeriya da ci biyu da ɗaya a wasa na ƙarshe da ya jagoranta, ya sa yanzu Nijeriya ce a ƙarshen teburi a rukuninta ne neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Bayan raɗe-raɗin da ake ta yi, da kuma sa hannun Ministan Wasanni na ƙasar, yanzu an ware mutum biyu da za a zaɓa ɗaya a cikinsu: Janne Andersson ɗan Sweden da Herɓe Renard ɗan Faransa.
Sai dai ko ma wane ne ya zama sabon kocin, ya san da sanin cewa lokaci na ƙoƙarin ƙure wa Nijeriya, kasancewar za a fara wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka a ranar 7 ga Satumba.
