Manchester United ta kusan kammala cimma yarjejeniya kan ɗan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 23 daga Paris St-Germain.
PSG ba ta da wani tanadi na ƙara kuɗin tayin Ugarte kan fam miliyan 51.
ɗan wasan gaba na Arsenal mai shekara Charlie Patino na dab da zama ɗan wasan Deportiɓo La Coruna.
Fulham ta amince da yarjejeniya da Lyon kan ɗan wasan Faransa mai shekara 21 Rayan Cherki.
Chelsea ta yi wa Manchester United tayin ɗan wasan baya na Ingila Ben Chilwell mai shekara 27 bayan shaida masa cewa ba ya cikin tsarin – Enzo Maresca.
West Ham na son sayen ɗan wasan tsakiya na Sifaniya mai shekara 27 Carlos Soler daga Paris St-Germain amma dole sai ta rabu da wasu ’yan wasan kafin ta samu zarafin sayensa.
ɗan wasan baya na Brighton ɓalentin Barco, mai shekara 20 na shirin komawa Sevilla a matsayin ɗan wasan aro.
Daraktan Napoli Giovanni Manna ya koma Ingila domin ci gaba da tattaunawa kan ɗan wasan tsakiya na Brighton da Scotland Billy Gilmour, mai shekara 23, da ɗan wasan gaba na Chelsea da Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 31 da kuma ɗan wasan tsakiya na Manchester United da Scotland Scott McTominay.
Watford ta amince ta karɓi aron ɗan wasan gaba na Bournemouth mai shekara 21 Daniel Jebbison.
Tsohon ɗan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 29, yana son ci gaba da taka leda a gasar firimiya bayan sanar da shi rashin tabbas kan makomarsa a Chelsea.
Barcelona na nazarin ɗauko ɗan wasan Juventus da Italiya mai shekara 26 Federico Chiesa.
