Gwamnatin Katsina ta ƙaryata umarnin ƴan jiha su mallaki makamai

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta bayar da umarni ga ƴan jihar su mallaki makamai don kare kawunansu daga hare-haren ƴan bindigar daji a faɗin jihar.

Da ya ke hira da manema labarai a ofishinsa, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dakta Nasir Mu’azu, ya ce gwamnati ba ta bayar da umarni ga ƴan ƙasa fararen hula su mallaki makamai domin yaƙar ƴan ta’adda ba.

Maimakon haka gwamnatin Dikko Raɗɗa ta ɗauki jami’an tsaro na al’umma 7,000 waɗanda tuni bayan samun horo aka tura su ƙananan hukumominsu, domin tunkarar ƴan ta’addar.

Haka kuma, gwamnatin ta ɗauki ƴan banga da su ma ta tura su ƙananan hukumomin da suka fito domin taimaka wa sauran jami’an tsaro a ƙananan hukumomi takwas da ta’addancin ya yi ƙamari.

Kwamishinan ya kuma nuna gamsuwa ganin yadda jami’an tsaro ke gudanar da aikinsu musamman wajen zaƙulowa da taimakawa da bayanai kan ayyukan ƴan ta’addar.

Har’ilayau, Dakta Nasir ya ce yanzu babbar matsalar da ke akwai ita ce ta masu tsegumta wa ƴan ta’addar bayanai na mutane waɗanda suna nan a lungu-lungu na ƙananan hukumomin da rashin tsaro ya yi ƙamari.

Daga nan ya yi kira ga al’ummomin waɗannan yankunan da su taimaka wa jami’an tsaro wajen zakulo waɗannan ɓatagari.

Idan za a iya tunawa, a cikin makon da ya gabata ne, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa Dr. Mu’azu ya na kira ga ƴan Jihar Katsina da su tashi tsaye wajen kare kawunansu ta hanyar daina jin tsoron ƴan ta’addar daji waɗanda suka addabi al’ummomi a yankuna daban-daban na jihar ta Katsina.

By Babaji