Sai da aka biya Dala 200,000 kuɗin fansa, kafin a sako ni – Mawaƙi Gnewzy

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Fitaccen mawaƙin nan na Najeriya da aka yi garkuwa da shi, Emuemu Oghala Goodnews, wanda aka fi sani da Gnewzy, ya bayyana adadin kudin da aka biya domin a sake shi.

A kwanakin baya, Blueprint ta ruwaito cewa, a watan Afrilun 2024 ne aka sace mawaƙi Gnewzy, a hanyar Eklat a Ughelli, da ke Jihar Delta. Yayin da Obas9ice, manajansa, kuma ɗan uwansa ya tsira da kyar, kasancewar suna tare.

Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi Dilly Umenyiora, shugabar kamfanin rikodin nasa, ta hanyar imel inda suka buƙaci a biya su kudin fansa har dalar Amurka 200,000.

An saki mawaƙin ne a ranar 3 ga Mayu.

Da yake ba da labarin lamarin da ya faru a lokacin hira da HipTɓ, Gnewzy ya bayyana cewa an biya dala 200,000 don ‘yancinsa.

Ya kuma bayyana cewa, wadanda suka sace sun yi shiga irin ta kayan ‘yan sanda.

“An biya kuɗin fansa kimanin dalar Amurka 200,000. Lamarin ya faru ne a lokacin da na je rangadin gidan rediyo a Jihar Delta, wacce ita ce jihar da na fito, a Ugheli. A ranar Lahadi bayan kammala abinda ya kai ni, sai na ce bari na ɗan shirya biki na nishaɗantarwa. 

“Don hama duk mun shirya don bikin, kuma mun je, na yi wasa, sannan muka baro zuwa masaukinmu. Bayan wani lokaci, ɗan uwana ya ce, yana so ya tarbo wani. Sai kawai na ce me zai hana mu tafi tare.

“Mun je inda muke so mu ɗauko mutumin, amma mutumin bai amince mu dawo tare ba, a kan hanyarmu ta komawa gida, a daidai wani wurin juyawa sai ga mutanen da ke sanye da kakin ‘yan sanda sun sha gabanmu.

“Muna isa wani wuri, sai suka tsaya suka fitar da ɗan uwana waje, suka ce masa za su harbe shi, kafin su ce masa ya gudu cikin daji idan ba haka ba su kashe shi.

“A zato na, wasu ne ke yunƙurin amfani da ni don isa wurin maigidana.

“Sai suka rufe fuskata da wani abu, amma ba su doke ni ba, kuma sun ba ni abinci, saidai sun ce idan na yi yunƙurin yin wani abu, za su yi magani na.”

By ukarofi