Ƙwararru a fannin ɗaukar hoto sun yi Allah wadai na ƙarancin matan Arewa a harkar

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Da yake jawabi ga mahalarta taro a yayin wani taron horaswa na kwanaki uku da aka gudanar a Kaduna tare da tallafin Ideas and Global Academy (IDGA). Shahararren ɗan jarida mai ɗaukar hoto kuma wanda ya kafa kamfanin hotuna da yaɗa labarai na SMM Sani Muhammad Maikatanga, ya bayyana cewa, rashin shigar matan Arewa cikin wannan aikin ɗaukar hoto cikas ne ga samun nasarar aikin jarida musamman a yankin Arewacin Najeriya.

Ya kuma bayyana cewa, abin takaici ne yadda ake samun ƙarancin matan Arewa a aikin jarida na ɗaukar hoto a Najeriya.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa, wannnan lamarin, na da alaƙa da riƙo da al’adu da addini waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen daƙilie ayyukansu.

“Wannan horon da muka fara, wani yunƙuri ne na samarwa matan Arewa matsuguni a aikin jarida na ɗaukar hoto a Arewacin Najeriya. 

Haka kuma, a tsayin shekarun da muke cikin wannan aikin, ba mu taɓa samun wani gagarumin horo ga mata masu ɗaukar hoto kan aikin jarida da ɗaukar hoto ba a Arewacin Najeriya, kasancewar mun san cewa sauran sassan ƙasar nan na da mata da yawa da ke yin waɗannan abubuwa kuma suna samun nasara,” inji shi.

A cikin jawabinsa, ɗan jarida mai ɗaukar hoto na ƙasa da ƙasa Mista Afolabi Sotumbe ya bayyana amfani da Photojournalism a matsayin babban makami na ci gaban kafofin watsa labarai.

Ya yi magana kan amfani da ingantattun hanyoyin yaɗa labarai daga yan jaridan hoto da masu ɗaukan hoton hakika/tarihi masu tasowa zai bunƙasa yaɗa labarai, bayyana tarihi, jinkai da tarayya, bincike na jarida da bayyana al’adu a wannan yankin.

“Ya kamata ‘yan jarida masu ɗaukar hoto su bi ƙa’idodin da ke bayan hotuna masu magana don yin tasiri,” inji Mista Afolabi.

Baya ga haka, Mista Sadiƙ Adelakun a cikin nasa jawabin ya jaddada muhimancin fahimtar Photojournalism da dijital Media a cikin shekarun da ake amfani da fasahar wucin gadi wato, AI wanda ya wajabta yin bincike don tantance hotunan gaskiya daga waɗanda aka ƙirƙira da fasahar AI.

“A wannan zamani, wasu masu ɗaukar hoto sun ƙirƙiro tsarin kasala ta hanyar samar da shagna da alama ba gaskiya ba ne, waɗannan abubuwan sun sa sana’ar ta yi rikici da ‘yan jarida da masu rubutun ra’ayin yanar gizo.

Ya kuma ƙara da cewa, wannnan kan sa dole masu ɗaukar hoto su saka jajircewa, ƙirƙira, bayyanai ikon ba da labari, da tsarin lokaci.

Wasu daga cikin mahalarta taron Zahra’u Gambo lawan da Jamila Jamo, Khadijah Abubakar sun samu lambar yabo kan ɗaukar hoto a gasa da dama da aka gudanar, sun kuma bayyana cewa, horon ya daidaita tunaninsu daga ɓangaren Documentary da ya haifar da sha’awar zuwa ga aikin jarida.

A yayin horon, mahalartan sun gudanar da ayyuka na amfanuwa kamar ziyarar masarautar zazzau da shahararriyar kasuwar fanteka.

By ukarofi