Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Kula da Hannayen Jari ta Nijeriya (SEC) a ƙarƙashin Emomotimi Agama ta bayyana shirinta na bayar da lasisin musayar kuɗin intanet ga cryptocurrency a cikin ƙasar domin haɓaka harkar cryptocurrencies a cikin ƙasar.
A watan Yuni ne hukumar SEC ta Nijeriya ta ƙaddamar da wani sabon shiri da nufin gaggauta yin rijistar VASPS.
SEC ta kuma ba da sanarwar gyare-gyare ga dokokinta kan hada-hadar kuɗi ta intanet da dai sauran su.
Da yake magana yayin wata hira da Bloomberg, Emomotimi Agama, babban darektan SEC, ya ce hukumar na da niyyar bayar da lasisi na farko don haɓaka hada-hadar kuɗi ta intanet a wannan watan.
“Kasancewa mai sha’awar crypto da fintech, zan iya gaya muku ba tare da shakka ba cewa wannan zai faru da wuri fiye da yadda kuke zato,” inji Agama.
“Dole ne mu tallafa wa matasan ƙasar nan don samun damar cin moriyar da ta dace a fannin fintech.”
Agama ya ce, SEC na son samar da manhaja inda mutane za su iya yin waɗannan abubuwa, kuma muna iya samun duk bayanan da muke buƙata”.
“Abin da ba za mu lamunta ba shi ne amfani da cryptocurrency don taƙaita kuɗaɗen mu,” inji Agama.
