Wani mummunan lamari ya afku a aauyen Karkari da ke ƙaramar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano, yayin da wata bazawara da ’ya’yanta biyar suka mutu bayan sun ci ɗan waken da aka yi shi da lalataccen rogo.
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya jefa al’umma cikin jimami.
Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da, Alhakatu Abdulkarim da ’ya’yanta – Bashir, Firdausi, Hafsat, Usman, da Jamilu, sun kamu da rashin lafiya ne bayan sun ci ɗan waken, abincin gargajiyar Hausawa.
An shirya abincin ne ta hanyar amfani da lalataccen rogo, lamarin da ya haifar da mummunar yanayi wanda ya yi sanadin mutuwar dukkan iyalan su shida.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna, an garzaya da iyalan zuwa babban asibitin Gwarzo bayan sun ci abincin.
Duk da ƙoƙarin ceto rayukan su da likitocin asibitin suka yi, lamarin ya ci tura, inda suka ce ga garin ku nan.
Rundunar ’yan sandan ta fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mutuwar, inda ake sa ran rahoton likita daga asibitin zai yi karin haske kan lamarin. “Har yanzu muna jiran rahoton likita daga asibiti don gano musabbabin mutuwar mutane shida,” inji SP Haruna.
Lamarin da ya faru a ranar Alhamis din da ta gabata, ya girgiza al’ummar yankin. Wata bazawara mai suna Alhakatu Abdulkarim, wadda ita kadai ce ke da alhakin kula da ‘ya’yanta guda biyar, ta yi amfani da garin rogo da ya kare a cikin shirin cin abincin cikin rashin sani. Wannan mummunan kuskuren ya bar iyali, da kuma al’umma gaba daya, sun lalace.
Hukumomin yankin sun buƙaci jama’a da su sanya ido kan ingancin abincin da suke ci, musamman a yankunan karkara inda za a iya takaita samun sabbin kayan abinci. Rasuwar Alhakatu Abdulkarim da ‘ya’yanta na zama dan tunatarwa kan illolin da ke tattare da cin kayan abinci da ya lalace.
A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, al’ummar garin Karkari na nuna alhini kan rashin uwa da ’ya’yanta, waɗanda suka rasu.
