Wata tawagar ma’aikata daga ma’aikatar lafiya ta Jihar Kaduna da kuma hukuma lafiya ta duniya sun tabbatar da mutuwar yara uku sanadiyar cutar mashaƙo a anguwar Tukur Tukur da ke ƙaramar hukumar Zaria, Jihar Kaduna.
Tawagar ta samu jagorancin Dakta Jamo, wanda shine shugaban hukumar lafiya ta matakin farko a Jihar kaduna a yayin ziyarar domin tabbatar da lamarin.
Dakta Jamo ya bayyana cewa anguwar Tukur Tukur na ɗayan daga cikin wurare da su ka ƙi amsar rigakafi lokacin da ake yi.
Ya roƙi mutanen anguwar da su rinƙa amincewa da rigakafi domin kare yaransu da kansu daga wannan muguwar cuta.
