Tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson ya mutu

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A ranar Litinin ne tsohon kocin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila, Sven-Goran Eriksson ya mutu ya na da shekaru 76 bayan fama da rashin lafiya ta cutar daji.

Kocin wanda ɗan asalin ƙasar Sweden ne ya jagoranci ƙungiyar ƴan ƙwallon Ingila ne a tsakanin shekarun 2001 da 2006 inda ya yi nasarar kai ƙasar zuwa zagayen wasan daf da na kusa da na ƙarshe a gasar kofin duniya na 2006.

A watan Fabrairun shekarar 2023 ne ya ajiye ayyukan da suka shafi harkar ƙwallon ƙafa sakamakon matsaloli na kiwo lafiyarsa.

By Babaji