Wata ƙungiyar Saudiyya ta kai Euro miliyan 65 don sayen Osimhen

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Ahli da ke ƙasar Saudiyya ta kai tsabar kuɗi har Euro miliyan 65 wa Napoli don sayen ɗan wasanta na gaba, Victor Osimhen.

Ana ganin Osimhen wanda ɗan wasan Super Eagles ta Nijeriya ne, zai bar ƙungiyarsa ta ƙasar Italiya a wannan kakar.

A ranar Lahadin da ta gabata ba a shigar da shi sahun ƴan wasan da suka fafata ba da ƙungiyar Bologna ba.

Rahotanni sun bayyana cewa, babu wata yarjejeniya tsakanin ɗan wasan da Al Ahli duk da cewa Napoli ta yarje masa ficewa daga gare ta.

Kawo yanzu dai zaɓi ya rage wa ɗan wasan wajen yin hukunci kan abin da ya ke ganin ya fi dacewa da shi.

By Babaji