Tinubu ya yi alƙawarin sauraron mabambantan ra’ayoyi – Shettima

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙudiri aniyar samar da ci gaba wajen kiyaye dokar ƙasa da bin tsarin mulkin karɓa-karɓa gami da sauraron mabanbanta ra’ayoyi da dokar Nijeriya ta amince da su.

Tinubu, wanda Mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilce shi, ya faɗi haka ne a taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) na shekara-shekara da aka yi a Legas.

Ya ce, gwamnatinsa tun farawarta, ta samu gagarumar nasara wajen sabonta ƙasa ta fuskar doka da gyare-gyaren tsare-tsarenta.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa ƙungiyar a ƙoƙarinta na jagorantar kundin demokraɗiyya da kuma kiyaye bin doka da oda a tsakanin al’umma.

Ya kuma yi kira ga lauyoyi da sauran al’ummar Nijeriya su haɗe hannu da gwamnatinsa wajen tabbatar da an samu ƙasar da kowa ke alfahari da ita.

Haka nan, Shugaban ya tabbatar wa al’umma cewa, tsare-tsare da matakai da gwamnatinsa ke tafiya akai zasu taimaka wajen samar da sauƙi ga al’umma duk da ƙalubale da ta ke fuskanta wajen sauya yadda abubuwa suke a baya.

Bugu da ƙari, Tinubu ya yi godiya ga kotun ƙoli kan yadda ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da shugabancin mai kyau da dokokin demokraɗiyya, ya na mai bada misali da hukuncin cin gashin-kai ga ƙananan hukumomi a Nijeriya da kotun ta yi a baya-bayan nan.

Daga ƙarshe, ya yi alƙawarin cigaba da bai wa harkar Shari’a goyon baya a matakan da suka dace tare da kira ga lauyoyi su tabbatar da kiyaye tsarin ayyukansu gami da yaƙar rashawa a kowane mataki.

By Babaji