An kama ƴan fashi kan zargin sojan-gona na ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumomin kiyaye doka na jihar Legas sun kama wasu mutane biyu da ake zargin su da fashi sanye da kayan ƴan sanda a yayin wani atsaye a jihar.

Wani ɗaukar bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda ƴan sanda suka gurfanar da waɗanda ake zargin ɗauke da makamansu da wasu ababe da ke nuna cewa ƴan fashi ne inda wanda aka jiyo muryar ɗaukar ta na cewa sun sanya kayan ƴan sandan ne da ke ɗauke da muƙaman Sufeto don fashi ga mazauna jihar.

Kawo yanzu babu wani saƙo daga rundunar ƴan sandan jihar game batun.

Sai dai hakan ya haifar da cecekuce acikin al’umma ganin yadda rashin aminci game da tsaro ke ƙara ƙamari.

Kazalika, Lamarin na da alaƙa da wani rahoto da ‘SaharaReporters’ ta fitar a watan Nuwamban 2022 inda wasu ƴan sanda masu sunaye Sufeto Saratu, Joy da Shehu a hedkwatar rundunar a Abuja suka bai wa waɗansu masu neman aikin ƙaramin ɗan sanda takardun bada aiki na bogi.

Faruwar ire-iren hakan sun sanya alamar tambaya game da lamarin ɗaukar aikin ɗan sanda da kuma hanyoyin bayyana kai a hukumar ƴan sanda.

By Babaji