Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Ƙasar Indonusiya ƙarƙshin shugabancin Dr H. Usara jakadanta a Nijeriya da haɗin gwiwar majalisar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Jihar Kano da ake kira KASCOTE ƙarƙashin shugabanta Alhaji Hassan Tahir Yaro, ta yi gagarimin taron bajekolin kamfanoni sama da 60 na wajen ƙasar nan musamman kamfanonin ƙasar Indonusiya da wasu ƙasashen Afirka, da kamfanonin gida Nijeriya.
A taron bajekolin irinsa na farko a tarihin Kano da aka fara ranar Talata aka kammala a ranar Asabar ɗin nan a titin Magajin Rumfa da ke Kano, a jawabinsa shugaban KASCOTE Hassan Tahir Yaro ya ce na da alfunu ga ɗaukaci al’ummar ƙasar nan ta fuskar bunƙasar tatalin arziƙi da yauƙaƙa zumunci da bunƙasar kasuwanci a tsakanin Nijeriya da sauran ƙasashen da kamfanonin da suka halarci taron, kana ga kuma dama ta ɗalibanmu za su samu na goraben karatu kyauta a ƙasar Indonusiya kamar dai yadda Alhaji HassanTahir ya bayyana a filin bajekolin A Kano.
Shi kuwa Dr Muhammad Ibrahim, shugaban gudanarwa na Kamfanin Alhaƙƙ Alamin Outlet Ltd, ma su shigo da ɗaukacin kayan buƙatun gida da sauransu daga ƙasar indunusiya, ya ce wanan taro nasu sun samo nasara 95 cikin 100 a wanan bajekoli na kayayakinsu na ƙasar Idonusiya, kasancewar da a Legas, za a yi amma aka dawo da toron Kano cibiyar kasuwanci wanan babar nasar ce ga Alhaƙƙ Alamin, a cewar Dr Muhammad Ibrahim Alhaƙƙ.
A ƙarshe Jakada Dr H Usara da ƙasar Indonusiya mai barin gadu, Amb Usuman A Ogan, gamsuwarsu suka nuna ga wanan bajekoli na ƙasa da ƙasa a Kano, inda Dr. H Usara ya ƙara da cewa Nijeriya da ƙasar na da kyakkyawar dagantaka da Nijeriya ta fuskar kasuwanci, al’adu da addini da sauransu.
