Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa ta jaddada aniyarta na inganta gudanar da halaltacciyar kasuwanci ta hanyar tabbatar da tsaron kan iyaka.
Kwanturola Janar na hukumar Bashir Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a wajen bikin ƙaddamar da wani ofishin kasuwanci a Kano tsakanin Nijeriya da Jam’iyyar Benin.
Kwanturola Janar na ƙasa da Mataimakinsa Sambo ɗangaladima ya wakilta ya ce an ƙaddamar da ofishin kasuwanci ne a matsayin wani babban tsari na inganta harkokin kasuwanci da haɓaka kasuwanci tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin.
Ya ƙara da jaddada ƙudirin Hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa na aiwatar da manufofin Gwamnatin Tarayya don samun ci gaban kasuwanci da tattalin arziƙi.
Ya yi nuni da cewa ƙaddamar da ofishin kasuwanci wani muhimmin mataki ne na sake buɗe kan iyakar Tsamiya dake a jihar Kebbi.”
“Ofishin zai daidaita hanyoyin kasuwanci, da kafa tashar fitar da kayayyaki na tsandauri don tallafawa masana’antu na cikin gida.”
ɗan Galadima ya ce “wannan matakin ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Tarayya na magance matsalar abinci da kuma ƙarfafa dangantakar tattalin arziƙi a cikin Najeriya da kuma kan iyakokinta.”
Shi ma wakili da ya wakilci kwanturola Janar ta Jamhuriyar Benin Idris Umar ya yaba wa shugabannin Nijeriya da Jamhuriyar Benin bisa amincewa da wannan tsarin don sauƙaƙa harkar kasuwanci tsakanin ƙasashen.
Da suke tsokaci game da buɗe ofis ɗin na kasuwanci tsakanin Nijeriya da jamhuriyar Benin shugaban ‘yan kasuwar Nijeriya Alhaji Bature Abdul’azeez da shugaban dattawan kasuwar Sabongari da Singa, Alhaji Ibrahim ɗanyaro sun yaba wa irin ƙoƙari da Sanata Isah Inuwa na jamhuriyar Benin wajen tabbatar da ganin an samar da ofishin.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an hukumar hana fasa kwauri ta ƙasa da wakilai na jamhuriyar Benin da shugabannin ‘yan kasuwa na Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.
Gwamnatin Kebbi ta fara rushe gine-ginen kan hanya da ba a yi su bisa ƙa’ida ba
Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta ƙuduri shirinta na inganta yanayin tsarin hanyoyin da ke cikin manyan garuruwa a jihar ta hanyar rushe duk wata gini da aka yi a kan hanya ba bisa ƙa’ida ba.
Hajiya Hafsat Ibrahim Tune Argungu, Babbar Sakatare a ma’aikatar Physical Planning ta jihar ce ta bayyana haka a garin Birnin Kebbi lokacin da hukumar ta ƙaddamar da rushe waɗansu gine-ginen a kan hanyar Jega da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
Hajiya Hafsat Ibrahim ta bayyana cewa aƙalla an gargaɗi duk mutanen da abin ya shafa tare da ba su wa’adin wata ɗaya da kwashe nasu ya nasu su bar wajen amma suka ƙi, saboda haka gwamanti ta ɗauki wannan matakin na ba sani ba sabo.
Ta ƙara da cewa duk da ya ke ana cikin mulkin dimukuraɗiyya ne gwamnati ba za ta zura ido mutane suna yin sonrai ba, saboda haka duk wanda ya yi wani gini a kan hanya idan bai cire ba hukumar za ta cire da kanta.
ɗaya daga cikin amfanin yin haka shi ne yana rage yawan haɗurra ga masu ababen hawa da kuma samun wadataccen fili don shan iska musamman a wannan zamanin na cuce-cuce suka yi yawa.
Ta ce mafi yawancin waɗanda wannan dokar ta faɗawa sun haɗa da masu shaguna ne da gidajen mai da kuma ɗaiɗaikun gidajen da ke kan manyan hanyoyi waɗanda akasarinsu na manyan mutane ne.
Ta kuma bayyana cewa wannan aikin na ba sani ba sabo aiki ne na haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatun filaye da gidaje da kuma ta tsare-tsare zai cigaba har illa Masha Allahu saboda haka tana kira ga waɗanda abin ya shafa da su yi gaggawar yin abinda ya kamata kafin aikin ya kawo kansu.
