
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban kamfanin BUA, Abdussamad Rabi’u ya ce dilolin siminti ne suka lalata masa shirinsa na sayar da buhu a Naira 3,500 ga al’umma a shekarar da ta gabata.
A lokacin da ya ke magana a zaman kamfanin karo na 8 a Abuja, Rabi’u ya ce yayin da kamfaninsa ke sayar da sama da tan miliyan guda ga diloli akan N3,500 da zimmar kwastomomi su samu rahusa, sai gashi dilolin na sayarwa akan N7,000 da N8,000.
Ya ce, don haka ne kamfanin ta dakatar da tsarin saboda ba dilolin ta nufi su samu tallafin ba.
Ya ƙara da cewa, kamfanin BUA ba zai dakatar da dilolin ba saboda su na samun riba mai kauri, domin kamfanin ba shi da ikon daidaita farashi a kasuwa.
Shugaban kamfanin ya kuma ce, rugujewar Naira da cire tallafin man fetur a Nijeriya ya taimaka wajen kawo cikas na gudanar da tsarin nasa.
“Da dama daga cikin dilolin suna amfani da damar tsarin. Madadin sayarwa a farashi mai rahusa ga kwastomomi, sai su ke sayarwa a sama da ninkin yadda muka sayar mu su.”
