
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Aƙalla Naira biliyan 1.04 ne aka biya masu garkuwa da mutane a matsayin kuɗin fansa acikin shekara guda a Nijeriya, kamar yadda rahoton hukumar leƙen asiri ta SBM ta ruwaito.
Cikin rahoton da hukumar ta fitar wanda hakan ya faru ne a tsakanin watanni Yuni na 2023 da Yuli na 2024, birnin tarayya Abuja ita ke da kaso mai tsoka yayin da Legas da Kaduna ke bi mata.
Yayin kamanta shiyyoyi, yankin kudu-maso-gabashin Nijeriya ke da kaso mafi tsoka wajen biya da kuma karɓar kuɗin fansa.
Hukumar tace, binciken nata ya gano cewa a tsakanin lokacin da ta zayyana, aƙalla mutane 7,568 ne aka yi garkuwa da su a hali 1,130, a sassa daban-daban a Nijeriya.
Rahoton ya ƙara da cewa, cikin jimillar Naira biliyan 10.9 da masu garkuwa da mutane suka buƙaci a biya su, Naira biliyan 1.04 suka samu wanda hakan ke nuna koma baya acikin harkokin nasu.
Jihohin da suka fi yawan adadin lamuran garkuwa da mutane sune Zamfara, Kaduna da Kastina inda aka yi nasarar sace sama da mutum 3,800 wanda kuma a yankunansu ne aka fi samun yawaitar mutuwar fararen hula.
Bugu da ƙari, ya ce aƙalla sai an rasa rai duk lokacin da aka samu lamarin yunƙurin garkuwa da mutane.
Cikin ababen da ƴan ta’addar ke buƙata a lokacin da suka yi garkuwa mutane akwai ƙuɗaɗe, abinci, abin sha da kuma taba a yankin Kudu yayin da a Arewaci su kan buƙaci a saya mu su babura.
