
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar Kula da Ɗalibai masu Hidimar Ƙasa, NYSC tace waɗanda suka yi karatu a makarantun Polytechnics ba tare da gabatar da takardar shaidar yin horon IT ba, ba za a yi mu su rijistar shiga sahun masu hidima ba.
Daraktar riƙon ƙwarya ta hulɗa da jama’a ta hukumar, Misis Carolina Lembu tace takardar shaidar kammala IT tana ɗaya daga cikin sharuɗan yin hidimar ta shekara ɗaya ga ɗaliban na Polytechnics.
A kwanakin baya ne NYSC ta fitar da sanarwar tsarin gabatar da takardar IT daga ɗaliban makarantun ‘Polytechnics da Monotechnics’ a matsayin rukuni na zama ɗan hidimar ƙasa musamman a harkokin sansanin hukumar.
A ranar 3 ga watan Agusta, 2024 ne Shugabar hukumar ta reshen jihar Legas, Yetunde Baderinwa ta bayyana hakan a matsayin doka ga ɗaliban inda ta ce hakan zai fara aiki ne daga ɗiba na gaba.
Tuni dai a ranar Alhamis, Misis Lembu tace dokar ta fara aiki inda sauran jihohi suka bi sahun waɗanda suka zartar da dokar wadda aka aiko daga hedkwatar hukumar da ke Abuja.
