
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Aƙalla ƴan ta’adda 37 ne aka kashe a ƙauyen Matusgi da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar jihar Zamfara, bayan da aka yi wani kiciɓis tsakaninsu da mazauna yankin a lokacin da suka yi yunƙurin garkuwa da mutane.
Wani mazaunin yankin ya ce, ƴan bindigar sun yi tururuwa ne akan babura da misalin ƙarfe 2 na ranar Laraba, ya na mai cewa sun sha yin karo da su amma wannan shi ne karo na farko da suka lallsa ƴan ta’addar.
Ya ce, sun shigo ƙauyen ne inda suka yi ta harbe-harbe wanda ƴan yankin suna sane da farmakin nasu inda hakan ya basu damar yi mu su zobe tare da lallasa su da makamansu na gargajiya.
Da farko dai ƴan bindigar sun ja da baya kasancewar an kashe mambobinsu guda goma.
Bayan haka ne, sai suka dawo a karo na biyu wanda hakan ya bai bai ƴan ƙauyen nasarar sake kashe wasu daga cikinsu inda aka samu jimillar mutuwar 37 daga cikin ƴan bindigar.
Hakimin yankin, Alhaji Ciroma Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce mutane uku daga cikin mazauna ƙyauyen sun rasa rayukansu a yayin artabun.
Ya ce, ƴan ƙauyukan maƙofta sun ce sun ga ƴan ta’addan ɗauke da gawawwakin mambobin nasu da aka kashe akan babura bayan faruwar al’amarin.
Ya ƙara da cewa, wannan shi ne karo na 13 da ƴan bindiga ke kai hari ƙauyen, inda sati uku da ya gabata suka yi garkuwa da mutane 23 wanda mafi yawancin su mata ne.
Sakamakon haka ne suka buƙaci a biya 150,000 ga kowane ɗaya daga ciki inda bayan an biya su kuɗaɗen, sai suka sako mata bakwai yayin da har yanzu su ke riƙe da sauran.
