Napoli ta amince ta sayar da Osimhen ga Saudiyya

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli da ke ƙasar Italiya, ta amince ta sayar da ɗan wasanta na gaba, Victor Osimhen ga ƙungiyar Al-Ahli ta ƙasar Saudiyya bayan ƙulla yarjejeniya.

An samu yarjejeniya tsakanin ƙungiyoyin ne kan biyan Euro miliyan 75 zuwa 80 don sayen ɗan wasan Nijeriyan.

Osimhen zai rattaɓa hannu a kwantiragin shekara huɗu akan albashin fam 646,154 a duk sati ba tare da biyan haraji ba kamar yadda ƙwararren ɗan jaridar ƙwallon ƙafa, Fabrizio Romano ya ruwaito.

Tuni dai ƙungiyar ta shirya gudanar da gwajin lafiya wa ɗan wasan wanda ke ƙoƙarin gujewa ƙungiyar Chelsea wadda ita ma tana cikin masu neman sa.

By Babaji