
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero ya sha alwashin cigaba da gwagwarmayar tabbatar da zartar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.
Hakan na zuwa ne bayan amsa gayyatar rundunar ƴan sanda kan zargin sa da hannu acikin ayyukan ta’addanci da suka haddasa taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya.
Ya ce, hakan da rundunar tayi masa ba zai sa ya karaya ba a ƙoƙarinsa na tabbatar da batun mafi ƙarancin albashi a Nijeriya da shugaban ƙasa ya amince da shi ya fara aiki, ya na mai cewa hakan ɗaya ne daga cikin ƙalubale da su ke fuskanta a yayin ayyukansu.
Ya ƙara da cewa, yadda su ka yi ta gwagwarmaya kan cimma matsaya game da ƙarancin albashi, haka zasu cigaba don ganin an zartar da shi kamar yadda gwamnatin tarayya ta ɗauki alƙawari.
Ya kuma yi godiya ga NLC, NAC, NEC da CWC ganin yadda suka bashi goyon baya a lokacin da aka aiko masa da saƙon gayyatar.
