
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sanannen dillalin miyagun ƙwayoyi Salisu jibril ɗan shekara 35 da haihuwa da ke zaune a garin Oni Yasu a karamar hukumar Rimi ya shiga hannun jami’in ƴan sanda a garin Katsina.
‘Yan sandan da ke aiki a ƙaramin ofishinsu da ke sabon Gari a cikin garin Katsina suka yi nasarar kama shi bayan ya yi ƙoƙarin tserewa.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar ƴan sanda a Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da ya ke gabatar da wanda ake zargi da aikata laifin.
ASP Sadiq ya bayyana cewa an samu Salisu jibril ɗauke da 1,330 na ƙwayoyi da suka haɗa da Tiramol da Fakiti na Lara da shima ƙwayar ne mai rikitar da ƙwaƙwalwa.
Ya bayyana hukumar ƴan sandan na cigaba da bincike wanda da zarar ta kammala, za ta gurfanar da wanda ake zargi da laifin gaban ƙuliya.
Har’ilayau, jami’in yaɗa labaran ƴan sandan ya sanar da kama wasu gungun matasa da suka ƙware wajan satan babura.
