Tinubu ya jajenta wa mutanen da ambaliya ta afka wa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa kan yadda ambaliya ta lalata wasu garuruwa da amfanin gona a sassan ƙasar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya nuna damuwa ga iyalan da suka rasa makusantansu, manoma, garuruwan da suka lalace da kuma waɗanda suka rasa dukiyoyinsu.

Wani bincike da hukumar bada agaji ta gaggawa, NEMA ta yi a kwanan nan ya nuna cewa, an rasa rayuka da dubunnan filayen noma da suka lalace da kuma dubunnan al’umma da suka rasa matsugunansu a faɗin Nijeriya.

Tinubu ya sake nanata buƙatar daidaita matsalolin ake samu da suka shafi muhalli ta yadda za a samu sauƙi game da aukuwar ambaliya acikinsu a ƙoƙarin gwamnatinsa na samar da walwala ga al’umma a muhallansu.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, za su cigaba da aiki da hukumomin da lamarin ambaliya ya shafa don ganin an bada tallafi ga waɗanda suka tsinci kansu aciki.

By Babaji