Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya buƙaci gwamnatin Nijeriya da ta bayyana dalilin da ya sa kamfanin Oando Plc mallakin ɗan gidan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya samu karɓuwar amincewar sayen kadarori na AGIP da ENI yayin da sauran kamfanonin hada-hadar mai irin su Shell da Mobil suma samu jinkiri.
Atiku ya kuma zargi gwamnatin ƙasar da baiwa Oando fifikon da bai dace ba a ɓangaren mai da iskar gas domin cutar da masu zuba jari da suka fi dacewa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu, ya caccaki gwamnatin Tinubu kan aiwatar da tsarin bada tallafi na bogi.
ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya caccaki majalisar wakilai kan rashin ɗaukar matakin da ya dace a kan kamfanin man fetur na Nijeriya, NNPCL, wanda ya ce ya ci gaba da “jinginar da kadarorin mai na kasa ga wasu muradu masu son rai.”
Atiku ya ci gaba da cewa, “A cikin watanni takwas kacal, hukumar da ke sa ido kan samar da kayayyaki ta Nijeriya, NUPRC, ta amince da wata yarjejeniya wadda ta kai ga karkatar da kadarorin ENI/AGIP da ke gabar teku zuwa Oando. A cikin wannan lokacin, Nijeriya ta janye dukkan karar da ake yi wa Shell/ENI a cikin badakalar OPL 245 a cikin abin da aka bayyana a matsayin ‘ƙuid pro ƙuo’.
“A bisa manufa, dimokuraɗiyya ya kamata ya zama gwamnatin jama’a, ta jama’a, da ta jama’a. Amma dimokuraɗiyya a Nijeriya ta zama gwamnatin Tinubu, ta Tinubu, da kuma ga Tinubu da ’yan uwansa.”
Atiku ya ƙara da cewa, “A watan Yulin 2023, majalisar wakilai, bayan amincewa da ƙudirin da Miriam Onuoha ta gabatar, ta umurci kamfanin NNPC da ya dakatar da sayen kadarorin OɓH har sai kwamitin ta ya gudanar da bincike.
