Gwamnatin Tarayya ta musanta ƙarin kuɗin makarantun sakandaren Unity

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ma’aikatar Ilimi ta yi ƙarin haske game da ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa makarantun sakandiren Gwamnatin Tarayya da aka fi sani da ‘Unity Schools’.

Wannan martanin ya biyo bayan wata sanarwa da ta yaɗu a kafafen sada zumunta musamman a ɗ, inda aka ce an buƙaci sabbin ɗaliban da za su shiga makarantun Unity su biya sama da N300,000, yayin da tsofaffin ɗalibai biya wasu ƙarin kuɗaɗen.

Takardar wacce ta jawo martani daga jama’a da kuma fitattun mutane irin su tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙoƙon aɗan Adam ta ƙasa (NHRC), Farfesa Chidi Odinkalu, ya nuna cewa Makarantun Unity sun aiwatar da ƙarin maƙudan kuɗaɗe ya bisa ƙa’ida ba.

Sai dai ma’aikatar ilimi ta ƙaryata waɗannan ikirari, tana mai jaddada cewa makarantun Unity na ci gaba da bayar da ilimi kyauta.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun Daraktar manyan makarantun ma’aikatar, Binta Abdulkadir, an bayyana takardar da aka yaɗa a matsayin “yaudara”.

Sanarwar ta jaddada cewa takardar ba ta samo asali daga ma’aikatar ba, kuma tana ƙunshe da kura-kurai da dama da suka haɗa da adireshi da ba daidai ba da kuma kura-kuran rubutu.

Sanarwar ta aara da cewa, “Mafi yawan kuɗaɗen da ɗalibai ke biya a makaratun Unity shi ne adadin Naira dubu ɗari (N100,000.00) kacal.”

“Wannan adadin ya shafi kuɗaɗen shiga, kayan makaranta, littattafan rubutu, littattafan motsa jiki, da sauran abubuwa na sabbin ɗalibai. Kuɗaɗen koyarwa a duk makarantun ya kasance kyauta ne.”

Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da sanarwar a matsayin wani yunƙuri na yaɗa labaran ƙarya da kuma haifar da ruɗani tsakanin iyaye da jama’a.

Ta shawarci duk wanda ke da damuwa game da kuɗin da aka amince da shi ya ziyarci gidan yanar gizon Ma’aikatar ko kuma ya tuntuɓi Makarantar Unity mafi kusa don samun ingantacciyar bayani.

A ƙarshe ma’aikatar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da takardar ƙarya, inda ta jaddada cewa makarantun Unity na ci gaba da bayar da ilimi mai rahusa, ba tare da wani ƙarin kuɗi ba kamar yadda takardar ta bogi ta nuna.

By ukarofi