Rundunar haɗin gwiwa sun shirya fafatawa da ‘yan ta’adda a Katsina            

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Haɗakan jami’an tsaro za su ɗauki tsawon wata guda suna kai wa ‘yan ta’adda hari ba tsayawa a wasu sassa, inda ya sa ‘yan ta’addan sukai kaka gida a jihar Katsina.

ƙananan hukumomin 19 cikin 34 da ke jihar za su fuskanci wannan arangama da zai ɗauki tsawon wata guda ba tsayawa.

Kwamishinan cikin gida da tsaro Dr Nasiru mu’azu Danmusa ya shaida wa manema labarai a Katsina, bayan kammala taron majalisar tsaro da Gwamna Dikko Raɗɗa ya jagoranta.

Dr mu’azu Danmusa ya ce majalisar tsaro ta ɗauki wannan mataki ne ganin yadda ‘yan bindiga ke amfani da yanayin damina suna ƙara zafafa hare-hare a wasu ƙananan hukumomi da ke jihar. 

Ya ƙara da cewa gwamnati ta samu rahotanni ƙaruwar munanan hare-hare na ‘yan bindiga da suke kashe mutane da garkuwa da wasu tare da sace dabbobinsu.

Kwamishinan sanar da ƙananan hukumomin da farmaki zai shafa ɓatagarawa, Batsari, Safana, ɗanmusa da Kankiya.

Sauran sun haɗa da Sabuwa, Dutsinma, Kurfi, ƙanƙara da Musawa.

Akwai kuma ƙananan hukumomin Matazu, Malumfashi, Danja, Bakori, Funtuwa da Charanchi.

Sai ya yi kira ga masu sarautun gargajiya da su taimaka wajen sanya al’ummarsu sa ido sosai idon suna da wasu biƙin ido da su gaggauta sanar da jami’an tsaro.

Harwala yau za su ci gaba da gudanar da addu’a na zaman lafiya.

Majalisar tsaron da aka faɗaɗasu sun haɗa da maynan jami’an sojoji da na ‘yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya da shugabannin ƙananan hukumomi.

Sauran sun haɗa da Hakimai, shugabannin ‘yan sanda na ƙananan hukumomi da ‘yan banga.

By ukarofi