Daga DAUDA USMAN a Legas
A ranar Litinin da ta gabata ne Allah ya yi wa Hajiya Salamatu Ibrahim Ɗanja rasuwa a sanadiyyar taƙaitacciyar rashin lafiya da Allah Ubangiji ya saukar mata a daidai wannan lokaci rasuwar ta marigaiyar hajiya Salamatu Ibrahim wadda ta girgiza ɗumbin al’ummar ƙaramar Hukumar ɗanja da ma na jihar Katsina baki ɗaya.
Hajiya Salamatu Ibrahim ɗanja ‘yar shekaru 75 ta rasu ta bar ‘ya’yanta guda biyar a duniya maza da mata, maza biyu mata uku da jikoki sama da hamsin. A cikin ‘ya’yan nata maza akwai Alhaji Aminu Lawal ɗanja wanda shine shugaban ‘yan kasuwa na ƙaramar Hukumar ɗanja da kewayenta gaba ɗaya. Da fatan Allah Ubangiji ya jiƙanta da rahama kuma ya gafarta mata zunubanta na duniya baki ɗaya.
Tuni dai aka yi zana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya a mincewa al’ummar Musulmi su yi idan hakan ta taso.
A yanzu haka dai al’ummar jihar Katsina da kewayenta gabaɗaya suna ta yin tururuwa zuwa ɗanja domin gabatar da ta’aziyyarsu ga Alhaji Aminu Lawal ɗanja da sauran iyalan marigayiyar gaba ɗaya.
Da yake tsokaci bayan gabatar da addu’ar kwana uku da rasuwar mahaifiyar tasa, Alhaji Aminu Lawal ɗanja ya ci gaba da nuna alhini tare da jimamin wannan rashi na mahaifiyar tasu da suka yi ya ƙara da cewa haƙiƙa shi da sauran ‘yan uwansa maza da mata sun yi babban rashi na mahaifiya mai son ci gaban ‘ya’yanta idan suka yi la’akari da irin tarbiyyar da ta ba su a lokacin da take raye.
Ya ce za su ci gaba da yi mata addu’o’i na musamman tare da fatan Alheri Allah Ubangiji ya jiƙanta da rahama kuma ya gafarta mata zunubanta na duniya a lahira.
Hakazalika ya cigaba da isar da saƙonsa na godiya ga ɗumbin al’ummar da suka fito daga sassa daban-daban na jihar Katsina da sauran ‘yan kasuwar na ƙaramar hukumar Danja waɗanda suka shigo garin ɗanja domin jajenta masa shi da sauran ‘yan uwansa dangane da rashin mahaifiyarsu da suka yi. Ya ce da fatan Allah Ubangiji ya saka wa kowa da alher.
