Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta nuna rashin jin daɗinta bisa ga yadda sojoji suka yi wa Sufurtandan ‘yan sanda Haliru Liman kuma DPO na ƙaramar hukumar mulki ta Wasagu da ke jihar Kebbi kisan gilla da sanyin safiyar Larabar da ta gabata.
Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ASP Yazid Abubakar da takwaransa na jihar Kebbi ASP Nafi’u Abubakar ya raba wa manema labarai ranar Larabar da ta gabata.
Takardar ta bayyana cewa sojoji da ke aiki wani shingen bincike OPHD Sector 6, Danmarke da ke ƙaramar hukumar mulki ta Bukkuyum a jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin wani Hassan ne suka harbe Sufurtandan ‘yan sanda Haliru Liman a kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take a wajen duk da kasancewar ya nuna musu katin shaidar shi jami’in ‘yan sanda ne.
Takardar ta ƙara da cewa jami’in ‘yan sandan yana kan hanyarsa ta zuwa Birnin Kebbi ne wajen taron wata-wata da ake a shalkwatar ‘yan sanda ta jihar Kebbi.
Wannan ɗanyen aikin gaskiya rundunar ‘yan sanda ba za su lamunce ba, bisa ga dukkan alamu akwai lauje cikin naɗi, saboda haka rundunar ‘yan sanda ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk matakin da ya dace don gano musabbabin wannan ɗanyen aikin. Ba shakka wannan ya saɓa wa dokar da ta yarda da aikin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro.
Takardar ta yi kira ga hukumomin da ke da ruwa da tsaki a cikin wannan lamarin da su bi hanyoyin da suka kamata don gano duk wanda ke da hannu a ciki don ɗaukar matakin da ya dace, duk da ya ke wannan shi ne zama silar rashin jituwa tsakanin jami’an tsaro ba, za su ci gaba da aiki tare kafaɗa-da-kafaɗa kamar yadda aka sani.
Daga ƙarshe takardar ta jajentawa iyalan marigayin tare da fatar Allah ya jikansa ya ba su haƙuri.
