Takarar 2027 ta fi ƙarfin Atiku —Bode George

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya bayyane cewa takarar Shugaban ƙasan 2027 a Jam’iyyar ta fi ƙarfin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

Cif Bode George ya ce Atiku Abubakar bai dace ya fito a 2027 ba, kamata ya yi ya janye wa wani daga yankin Kudu mai jini a jika.

Wannan na cikin sanarwar da George ya fitar ranar Laraba, yana jaddada cewa wajibi ne ɗan takarar PDP a 2027 ya kasance daga yankin Kudu.

Dalili a cewarsa, shi ne, “saboda yanayin Nijeriya da al’ummar ƙasar da kuma kundin tsarin mulkin PDP.

“A 2027 shekarun Atiku sun kai 81, don haka dole a lokacin dole ya yi koyi da Shugaba Joe Biden na Amurka, ya bar masu tasowa da jini a jika su shige ofishin shugaban ƙasa.

“Ba ni da wata matsala da Atiku, hasali ma abokina ne, amma idan gaskiya ta zole dole in faɗe ta; nan da 2027 shekarunsa sun haura 80.

“Ni dai da na haura shekaru 80, wane mulki ko muƙami zan tsaya nema? Shi ma Atiku abin da ya kamace shi ke nan.

“Kwanan dai mun dai ga yadda Shugaba Joe Biden na Amurka ya janye wa mataimakiyarsa Kamala Harris, ta yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe da ke tafe a watan Nuwamba.

“Hakan shi ne dattaku, kuma bin da ya kamata Alhaji Atiku Abubakar ya yi ke nan a 2027.

“Sai PDP ta tsayar da dan Kudu takarar kujerar shugaban ƙasa,” in ji George, wanda tsohon gwamnan Jihar Ondo ne a zamanin mulkin soja.

By ukarofi