Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Hukumar Kula da Kare Iftala’i da Agajin Gaggawa ta ƙasa NEMA, shiyyar Kano da Jigawa ƙarƙashin shugabancin Dakta Nurardeen Abdullahi, ta shirya gasar amsa tambayoyi ta hanyar wasa ƙwaƙwalwa ko a ce gasar kacici-kacici a tsakanin ɗaliban makarantun sakandaren Kano guda takwas da suka fafata a gasar da makaratu uku cikin takwas su ka yi nasara wajen amsa tambayoyi da NEMA ta shirya gasar akan alaƙar shara da nufin ilimantar da ɗaliban yadda shara ke haddasa ambaliyar ruwa idan ba a kiyaye ba, kamar dai yadda Shugaban NEMA shiyyar Kano, Jigawa, ya bayana a wajen gasar da aka yi a makarantar ‘yan mata ta GGSS Dala, Kano a ranar Litinin da ta gabata.
Haka kuma Dakta Nuredeen ya ce ɗaliban da suka amsa tambayoyin ya nuna cewa sun fuskanci ilimin da manufar shirya gasar don sanin alaƙar shara da ambaliyar ruwa, sai kuma alaƙar yawan jama’a da ambaliyar ruwa a wanda duk idan aka gane haka za a iya shawo kan matsalar kafin ta afku a bakin Dakta Nuredeen.
A ƙarshe dai an makarantar sakandare ta ‘yan mata ta GGSS Bullukiya kofin samun matsayi na uku a gasar wanda shugabar makarantar Bullukiya Hajiya Hannatu Adamu Gwaram ta bayyana farin cikinta da wannan rana.
Makarantar GGSS Dala ta karɓi kofinta a matsayi ta biyu a gasar ƙaƙarshin shugaban Ramatu M Tufa.
Sai makarantar sai kai ta Khalid Bin Walid, ƙarshin shugabancin Barista Ibrahim Abdulhamid da ta karɓi kofinta na yin nasarar zama ta ɗaya a gasar da NEMA da haɗin gwiwar SEMA ta Kano da NRCS ta shiryawa ɗaliban sakanduren Kano.
