Fitaccen ɗan wasan Nijeriya na farko a gasar Olympics, Nojim Maiyegun ya mutu yana da shekaru 84 a duniya.
Maiyegun ya kafa tarihi inda ya lashe lambar tagulla a dambem masara nauyi a gasar Olympics ta Tokyo a shekarar 1964, abin da ya ba shi matsayi a zauren wasannin ƙasar.
A cewar wani saƙon da wani masoyinsa, Rudolfine Soultan ya wallafa a Facebook, Maiyegun ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Soultan ya bayyana mutuwar Maiyegun a matsayin “abin baƙin ciki” kuma ya bayyana cewa suna shirin gudanar da bikin cika shekaru 17 tare cikin kwanaki biyu.
Nasarar ban mamaki da Maiyegun ya samu a Tokyo da lambar tagulla da ya samu a gasar Commonwealth ta 1966 a Kingston, Jamaica, ya zaburar da ‘yan wasan Nijeriya.
