Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Dubun duba tan mutane daga ciki da wajan Jihar Katsina suka halarci jana’izar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa marigayi Malam Umaru Musa Yar’adua duk da ruwan sama da akai ta yi.
Jana’izar da ta gudana a filin wasa na cikin garin Katsina kusa da gidan marigayiyar a unguwar Yar’adua da misalin ƙarfe 2.20pm na yammacin talata Sheikh Aminu Ibrahim yammawa ne ya jagoranci sallar.
A cikin waɗanda suka halarci jana’izar akwai mataimakin shugaban ƙasa Kashim shattima da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattijai sanata Ahmad lawan.
