Ni na fara rubuta littafi kan fasahar sadarwar da harshen Hausa – Abubakar Tsangarwa 

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Abubakar Muhammad Tsangarwa fitaccen marubuci ne kuma masanin da ya ƙware a kan harkar fasahar sadarwa. Ya yi wallafe wallafe da dama a kan harkar fasahar sadarwa kuma ya koyar tare da yaye dumbun jama’a da suka ƙaru da iliminsa wanda a yanzu haka wasu sun zama malamai a manyan makarantu suna bayar da ilimin fasahar sadarwar.

A cikin tattaunawar da jaridar MaNHAJA ta yi da shi, ya bayyana mana yadda ya fara harkar da kuma irin nasarori da kuma matsalolin da ya fuskanta. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatun mu.

ABUBAKAR MUHAMMAD TSANGARWA: To Assalamu alaikum. Farko dai sunana Muhammad Abubakar Tsangarwa, kamar yadda yake a Kasar Hausa, ni dai na tashi na samu kaina Ina zuwa makaranta da haka na tashi na yi wayo, saboda yawanci za ka ga kawai zuwa makaranta ake yi ba a ma san ana zuwa ba, sai a cikin makarantar ne mutum zai fahimci wannan makaranta ce. Kuma idan muka dubi abin da ya shafi shi karatun boko. Na yi karatun firamare kamar yadda kowa yake yi a makarantar firamare ta Tsangarwa, na gama a 1987 sai kuma na yi ƙaramar sakandare ta Gwaram da Busurka. Sannan na yi babbar sakandare a garin Wudil. Sai kuma na tafi makarantar horas ta malaman fasaha ta garin Bichi na samu takardar shaidar karatu ta NCE. Daga nan muka dawo gida a 1999 aka fara harkokin yadda za a dogara da kai, duk da a lokacin aikin koyarwa ba wahala yake ba, amma dai sai na zaɓi na ci gashin kaina tun a lokacin, saboda na auna na ga abin da ake karɓa da kuma buƙatar mutum ta yau da kullum, sai na haƙura.

Cikin taimakon Allah na karanta Lantarki ne, don haka sai na zo na fara harkokin haɗa wuta a gidajen mutane suna biya na. Sai kuma zuwa shekarar ta 2000 na fara harkar buga takardu, Wanda a nan na haɗu da kwamfiyuta. Don haka sai na ƙara komawa Jami’ar Tafawa Balewa a Bauchi na yi karatu na shekara guda a reshenta da ke Kano, in da a nan na samu difloma mai zurfi a kan Kimiyyar Kwamfiyuta, kuma tun daga wannan lokacin ne ita harkar kwamfiyuta ta ɗauki hankali na, saboda mutane suna kallon ta kamar wata aba ce mai wahala, don lokacin da na ce na tafi Jami’ar Tafawa Balewa na yi karatun kwamfiyuta har mamaki ake yi, saboda akwai lissafi a cikin karatun, Kuma ni cikin taimakon Allah tun da na tashi, duk karatun da babu lissafi ban cika son sa ba a gaskiya, domin Ina ɗaukar lissafi don ya fi burgeni sai kuma na ƙara da wanda yake ba lissafi ba na je na zana jarrabawa a cikin haka. 

To bayan na kammala karatun a Jami’ar Tafawa Balewa, sai kuma na shiga karantar da ilimin fasahar sadarwar da kuma idan aikin tafin ya samu na yi, duk da dai ba ni da tawa kwamfiyutar a lokacin sai na karɓi aikin tafin ɗin na je wani waje na yi, to haka na rinƙa yi ina aikin kwamfiyuta kuma ina koyar da ita, tun daga shekara ta 2000 har zuwa 2004, wanda kuma a lokacin ne na fara buɗe shago nawa a Tashar Dan dishe kuma a lokacin har na kai ga rubuta littafin kwamfiyuta wanda na saka wa suna ‘Kwamfiyuta A Sauƙaƙe’ wanda kuma shi ne littafi na farko littafin kwamfiyuta na Hausa da aka rubuta aka buga. Sai kuma na fitar da wata mujalla mai suna Fasahar Zamani.

To dukkan dalilan da suka saka na zaɓi na fara wallafe wallafe na da kuma rubuce rubuce na a kan ilimin fasahar sadarwar na kwamfiyuta kuma cikin harshen Hausa, shi ne abin da na yi nazari tun a wancan lokacin, mutanen mu ba wai iya matasa ba akwai matsalolin rashin aikin yi, sai kuma ita kwamfiyuta ta zo da cikakkun guraben aikin yi, wanda mutum yake da wadataccen lokacin sa, matuƙar dai ya naƙalceta, to za ka ga cikin taimakon Allah, ba zai rasa ɗan abin da zai kai bakinsa ba. 

To wannan sai ta sa na fara wallafe wallafe na da Hausa, a haka ina karantawa ina rubuce rubuce, kuma ina gyaran kwamfiyuta ina wucewa gaba mutane su saya, har Allah ya sa muka zo shekara ta 2009, na buɗe makaranta ta koyar da ilimin fasahar sadarwar ta kwamfiyuta tawa ta kaina a Unguwar Kabuga Janbulo, kuma dai a wannan gaɓar sai na ga akwai buƙatar a ci gaba da wayar da kan mutane a kan abin da ya shafi ilimin fasahar sadarwar na kwamfiyuta, don haka sai na je na samu gidan rediyon Freedom da ke Kano muka yi wani shiri da su wanda na saka wa suna Mu Koyi Kwamfiyuta, kuma shirin ya ɗauki hankalin jama’a, don ba na mantawa daga cikin hanyoyin da nake bi na samun bahasin abin da nake yi wata rana ina tafiya a kan mashin sai nake tambayar mai mashin ɗin ko ya san wani shiri da ake gudanarwa na mu koyi Kwamfiyuta?

Sai ya ce, shi bai taɓa tunanin zai iya koyar kwamfiyuta ba, sai da ya saurari wani shiri da ake yi a gidan rediyon Freedom. Har sai da muka yi nisa nake faɗa masa ai ni nake gabatar da shirin. To na samu abubuwa sosai na irin wannan wanda akwai waɗanda kullum sai dai addu’ar godiya, saboda na tabbatar akwai wanda aka haɗu da shi aka je wani waje aka ɗora hannunsa a kan harkar kwamfiyutar, a yanzu haka ba wai shi ba, na ƙarƙashin sa ma sun gina gidaje, da shi da ƙannensa da yayansa suna nan suna ci ta ƙarkashin koyar da su da na yi.

Kuma duk da haka na koma na ci gaba da karatu a Jama’ar Fasaha ta Minna, nan kuma na samu digiri a kan ilimin fasahar kwamfiyuta a reshenta na Kaduna. 

Daga nan dai na faɗaɗa bincike saboda na ga irin alfanun da ilimin yake da shi da kuma ƙarancin ilimin a Kasar Hausa, sai na yi tunanin yaranmu da suke zuwa Islamiyya a waɗansu gidajen sai muka ga waɗanda suke da dama wacce irin gudunmawa za mu iya ba su, don haka sai na ƙirkiri wata sot waya da na kira mai darasu wadda ita manufar ta shi ne tallafa wa koyar da ilimin addinin Muslumci, kuma mutane masu buƙata mutum idan ya dawo gida zai ɗan samu ya buɗe ya karanta wani darasi na addinin Muslumci cikin harshen Hausa, su kuma ɗalibai da suke jami’a za su yi amfani da ita wajen ɗaukar ayyuka kai tsaye, yadda an rage musu sauƙin rubutawa. 

Sannan su kuma masu haddar Alƙur’ani akwai wajen da mutum zai shiga ya rinƙa yin karatun da Kwamfiyuta, kamar abin da ake cewa muraja’a kenan, wato za ka karanta surar, sai ita ma Kwamfiyutar ta karanta maka ta gaba, sai ta tsaya kai karanta ta gaba, da haka da haka har za ku sauka.

To muka ƙaddamar da wannan fasahar a lokacin a ɗakin taro na Mambayya wanda Farfesa Abdallah Uba Adamu ya jagoranci gabatar da jawabi a wajen. 

Ta haka na ci gaba dai ina karatuna ina harkoki na wanda daga shekara ta 2010 sai na fara wallafa littattafai da za a koyar a matakin firamare, har zuwa 2015 na kammala rubuta littattafan Hausa guda shida wanda aka rinƙa karantar da su a makarantu. Sannan kuma na ɗora rubutun littafin daga matakin ƙaramar sakandare kuma Alhamdulillah a yanzu har na kai ga rubuta littafin a matakin babbar sakandare. Kuma duk da haka Ina ci gaba da menan ilimi har zuwa lokaci na gaba kuma a fannin koyarwa mun karantar da ilimin fasahar Kwamfiyuta da yara da kuma manyan mutane, shi ya sa za ka ga yawanci ko a soshiyal midiya za ka ga ana kirana da Malam, to wannan shi ne yake kawowa.

Dangane da rubutu. Ko za ka fada mana adadin littattafan da ka rubuta?

To na rubuta littattafai da dama kamar ‘Kwamfuta A Sauƙaƙe’ ‘Computer Studies Primary’, Kitabul Akhdhari- Arabic, Transliteration, Hausa da English, Computer Studies for JSS 1-3 guda 3, Computer Studies for West Africa SS 1-3 , Nahwulwadhi Hausa and English, Ishmawi Hausa and English, Kawa’idi Hausa and English. Da dai sauran su, don ina ganin na rubuta littattafai sun fi guda 20, kuma ina kan rubuta wasu ma nan gaba.

Za mu so ka yi banayi a game da ilimin fasahar sadarwar domin matasa su fahimci yadda yake.

Shi ilimin fasahar sadarwar, ilimi ne wanda a yanzu ake yin amfani da shi. Baya ana ƙiran sa ilimin fasahar sadarwa. Daga baya kuma sai aka zo ana kiran sa da Ilimin fasahar sadarwa da bayanai, kuma ilimi ne wanda a yanzu duniya take tunƙaho da shi, ko kuma ma ta ƙudiri aniyar ɗoruwa a kansa bakiɗaya zuwa mataki na gaba. Saboda haka amfanin sa ba zai lissafu ba, haka ma faɗin sa ba zai lissafu ba, saboda a kullum ƙara buɗe rassa yake yana ƙara faɗaɗa, tare da ƙara samar da damarmaki da guraben aikin yi.

Ba na mantawa a wasu lokuta a can baya, kamar 2005 zuwa 2006, duk littafin da na ci karo da shi, sai na ga mai littafin ya ce ilimin fasahar sadarwar yana kawo korar ma’aikata, kuma ya zo da sabanin guraben ayyukan yi. 

Amma ni a ra’ayina guraben da fasahar sadarwar ta kawo na aikin yi sun fi wanda aka rasa yawa, wannan ta sa a 2004, aka ba ni dama na gabatar da takarda, mai taken Kwamfiyuta da Guraben Ayyukan Yi, a ɗakin karatu na Murtala Muhammad. 

To ba za ka iya lissafa damarmaki na ayyukan yi a fannin kwamfiyuta ba. Kuma za ka ga a rubuce rubuce na za ka ji na ce maka ga guraben ayyukan yi nan fululu, ba wai iya kwamfiyuta ba ne. Saboda haka ilimin fasahar sadarwar da bayanai wannan zamanin sa ne, baya idan ana neman masu aiki za ka ga an ce mutum ana son ya samu ilimin gogayyar shekara kaza, amma ilimin kwamfiyuta yana da ƙarin dama a kan wancan, amma a yanzu dole ta zama larura sai kana da ilimin kwamfiyuta. 

A yanzu maganar da ake yi, ita duniyar ta nan gaba, duk waɗannan abubuwan da kake kallo, akwai abin da ake cewa duniyar gaibu wanda a baya da na ambaci wannan sunan sai da ya bai wa manyan masana mamaki. To a yanzu tanadin da turawa suka yi, shi ne suna son su ƙirkiri wata duniyar gaibu da za a rinƙa gudanar da abubuwan rayuwa, ba wai a zahiri ake yi ba. Misali a zahiri kamar yadda muka tashi a baya, idan kana so ka sayi abu za ka tafi kasuwa ko kanti ka saya. To yanzu kuma sai ya zama a rayuwa ta gaibu za ka je kasuwar ka yi sayayya ka kuma dawo gida ka zauna, a duk faɗin duniya kuma kayan ya biyo ka har gida. To wannan abin ake so a tabbatar.

Kamar kwanakin baya da ake ta cece ku ce wanda har yanzu ban samu lokaci na gama rubutu a kan abin da ya shafi masu kuɗin Cripto, kowa yana faɗar albarkacin bakinsa, wanda na so a lokacin na faɗa wa su masu harkar cewa su ci gaba da yi, domin su ne masu arziki a nan gaba, saboda yadda duniyar take komawa. Yanzu babban abin da ya dami Turawa a wannan fanni na Cripto shi ne harkar tsaro, ya zama za a samu hanyoyin da za a yi wannan hada hada ta kuɗaɗen da babu su, ka yi sayayya a kuɗin da babu shi a zahiri kuma ba tare da matsala ba, wannan shi ne babban abin da suka duƙufa a kansa kenan yanzu, suna nan suna dukkan wasu shirye shirye. Saboda haka shi ilimin fasahar sadarwar da bayanai, gaskiyar magana a yanzu zamanin sa ne, kuma yanda damarmaki da yawan da ba za mu iya ƙidaddige su ba, don haka duk wanda Allah ya ba shi dama ya tashi ya yi iya abin da zai iya yi don ya ga ya amfana da wannan dama ta fasahar sadarwar da bayanai.

Kuma ko babu komai ni a nawa ɓangaren sai godiyar Allah an ɗan yi abin da aka yi, don kamar yadda na faɗa a baya, ni na fara wallaf littattafai a kan ilimin fasahar sadarwar da bayanai da Hausa, sannan kuma na yi mujalla mai suna Fasahar Sadarwa, kuma akwai wani littafin da na yi niyyar yi wanda a yanzu na ɗan jingine shi sai zuwa nan gaba.

Ya kake ganin yadda matasan mu za su ci gajiyar ilimin fasahar sadarwar da bayanai a wannan lokacin?

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

By ukarofi