NLC ta yi watsi da ƙarin farashin man fetur da wasu kayayyaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta yi watsi da ƙarin farashin man fetur da na wutar lantarki a Nijeriya.

A lokacin da ya ke magana game da umarnin mayar da litar Naira 900 da NNPCL ta yi a jiya Talata, Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya ce hakan tsanantawa ce akan matsin da al’umma ke ciki.

Ya ce, sun amince da Naira 70,000 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata da sharaɗin ba za a ƙara farashin man fetur ba a matsayin ɗaya daga cikin yarjejeniyar amincewar tasu.

Ya kuma ce, shugaban ƙasa ya ba su zaɓin kodai a mayar da ƙarancin albashi N250,000 ta yadda litar mai za ta koma N1,500 zuwa N2,000, ko kuma farashin litar man fetur ya kasance a yadda ya ke amma mafi ƙarancin albashi ya zama N70,000.

Sakamakon haka ne ya ce sun amince da zaɓi na biyun don kar al’umma su shiga cikin wani sabon ƙunci a gaba.

Ya ƙara da cewa, yin hakan hakan yaudara ce kuma abu ne da zai ƙara ƙuntata wa al’umma duk da tattaunawa da su ke yi da gwamnatin game da matsalolin da hauhawar farashin man ke haifarwa a ƙasa.

By Babaji