Sabon jadawalin gasar zakarun Turai na 2024/25

Spread the love

Gasar zakarun nahiyar Turai ta dawo a wannan kaka ta 2024/2025, amma ba kamar yadda yake a baya ba, saboda an samu sauyi sosai. Wasu sauye-sauyen dai masu sauƙin fahimta ne, wasu kuwa akwai sarƙaƙiya.

Da farko dai wannan ne karo na farko a cikin shekaru 21 da aka sau sauyi a tsarin gasar zakarun Turai. Daga shekaru 21 da suka wuce zuwa wannan kaka, ƙungiyoyi 32 ne ke fafatawa a wannan gasa, kuma an kasa su ne zuwa cikin rukunnai 8 mai ƙunshe da tawaga 4 ko wanne. Tawagogi 2 da suka fi samun maki a kowane rukuni su ne za su tsallaka zuwa zagayen ƙungiyoyi 16 na sili ɗaya ƙwale, kana waɗanda suka zo na 3 za su fafata a gasar zakarun Turai ta Europa, waɗanda suka zo na 4 kuma sun fice daga gasar kenan.  

Yanzu ƙungiyoyi 36 za su fafata a wannan gasa akasin 32, amma kuma ba za a kasa su zuwa rukuni-rukuni ba. A maimakon haka, an bi tsarin lig, inda yawan makin da ƙungiya ta tara ne zai fishe ta.

An baza ƙungiyoyi 36 a  cikin tukwane 4 mai tawagogi 9 kowanne. Ko wacce tawaga za ta fafata da tawagogi 2 daga kowane tukunya, ɗaya a gida, ɗaya a waje.

Babu ƙungiyar da za ta fafata daga wadda ta ke ƙasa ɗaya da ita, kana kowace ƙungiya za ta iya gwabzawa ne kawai da ƙungiyoyi 2 daga ƙasa guda.

A baya, a watan Disamba ake kammala wasannin matakin rukuni, amma yanzu za a kai watan Janairu.

Yanzu wasanni a gasar sun ƙaru daga 96 zuwa 144.

– ƙungiyoyin da suka kammala a matsayi na 25  zuwa 36 za su fice daga gasar a watan Janairu.

– Waɗanda suka kammala a matsayi na 9 zuwa 24  za su buga wasannin cike gurbi, wato playoffs a watan Fabrairu, don samun shiga zagayen ƙungiyoyi 16 na sili ɗaya ƙwale.

Waɗanda suka kammala a matsayi na 1 zuwa na 8 kuwa za su samu zuwa zagayen ƙungiyoyi 16  wanda za buga a watan Maris kai tsaye ba tare da sun buga wasannin cike gurbi ba.

ƙungiyoyi 36 za su raba yuro biliyan 2 da miliyan ɗari 6, akasin baya, inda ƙungiyoyi 32 ke raba yuro biliyan 2.2.

By ukarofi