Ban tattauna da wata ƙungiya ba a kan barin Man City – De Bruyne

Spread the love

ɗan wasan ƙungiyar Manchester City, Keɓin Bruyne ya bayyana cewa shi bai magana da wata ƙungiya ba a kan barin ƙungiyar a bana.

ɗan wasan na ƙasar Belgium ya bayyana cewa “ƙofarsa a buɗe take” sannan ya tattauna da iyalansa a kan yiwuwar barin Manchester City bayan an bayyana cewa wasu ƙungiyoyin a Saudiya na zawarcinsa a ƙarshen kakar bara.

De Bruyne mai shekara 33 ya koma Manchester City ne a shekarar 2015 daga Wolfsburg ta Jamus, shekara ɗaya gabanin zuwa Pep Guardiola.

Gurdiola ya sha bayyana a watannin baya cewa ba za su sayar da De Bruyne ba, sannan yanzu shi ma ɗan wasan ya fito ya bayyana cewa shi bai taɓa tattaunarwa da wata ƙungiya ba a kan barin ƙungiyar.

“Maganar gaskiya ban yi magana da wata ƙungiya ba,” inji De Bruyne a tattaunawarsa da BBC Radio Manchester.

By ukarofi